Buhari ya jefa Najeriya cikin tsaka-mai wuya

– Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti ya kara sukar Gwamnatin Shugaba Buhari
– Fayose yace Shugaba Buhari ya jefa Najeriya a cikin wani mawuyacin hali
– Gwamna Fayose yace ana nema a ga bayan Fastoci
Buhari ya jefa Najeriya cikin tsaka-mai wuya
Buhari ya jefa Najeriya cikin tsaka-mai wuya
Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose yace Shugaba Buhari ya jefa Kasar nan cikin wani irin hali. Ayo Fayose ya zargi Shugaba Buhari da kokarin kama Fasto Sulaiman Johnson a wata hira da yayi da Jaridar Guardian.

Fayose yace dama ya gargadi mutane game da Buhari, ga shi yanzu babu wanda ya tsira; daga ‘Yan siyasa zuwa Alkalai, da ‘Yan Jarida har Limaman coci. Hukumar DSS dai tana neman Fasto Sulaiman Johnson bayan yayi kira ga mabiyan sa da su yanka Fulanin da suka gani kusa da Cocin sa.
Fayose yace har Sanatocin APC dai sun gaji da Buhari don kuwa sun ki amincewa da nadin Magu na EFCC da kuma yunkurin rufe filin jirgin sama na Abuja dama wasu batutuwan irin su rokon a kori sakataren gwamnati Babachir Lawal.
Haka nan shi kuma Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya sha alwashin kare gaskiya da yin adalci. Osinbajo ya fadi wannan yana mai mayar da martani ga Kungiyar CAN da suka soki tsit din da yayi game da abin da suke gani na hari da ake kaiwa Fastoci.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook
Post a Comment

Popular posts from this blog

BellaNaija Weddings presents #AsoEbiBella – Vol. 178 – The Latest Aso Ebi Styles

BN Bridal: BERTA Bridal Fall 2017 Collection

Weddings presents #AsoEbiBella – Vol. 168 – The Latest Aso Ebi Styles